Da zafi-zafi: Lionel Soccoia ya raba gari da Kano Pillars

By TangaSports Ɗan ƙasar Faransa, Emmanuel Lionel Soccoia, ya ajiye aikin sa na mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars watanni 5 da sanya hannu a kwantaragi na tsawon shekara guda. Tsohon mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafar na Black Leopard ta ƙasar Afirka ta Kudu, ya sanya hannu ne a kwantaragi na shekara guda a watan Oktoban bara, a shirye-shiryen fara wasannin zagayen fidda gwani na gasar Ajin Ƙwararru ta Afirka, CAF Confederation Cup, da ASC Jaraaf ta ƙasar Senegal. Kafar yaɗa labarai ta www.sportsdaily.com.ng ta gano…

Read More

Sanusi Ibrahim ya sauya sheƙa zuwa Montreal Impact a gasar MLS

TangaSports Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nasarawa Utd, Sanusi Ibrahim ya sauya sheƙa zuwa ƙungiyar Montreal Impact ta ƙasar Kanada daga 36-Lions. A ranar Talata ne matashin ɗan wasan ya sanya hannu a kwantaragi da Montreal Impact zuwa shekarar 2023 tare da alƙawarin tsawaita zaman sa a ƙungiyar zuwa 2024. A kakar 2018/19 ne Sanusi ya lashe takalmin zinare a lokacin yana wakiltar ƙungiyar ƙwallo ƙafa ta Nasarawa Utd bayan ya zura ƙwallaye 10 a wasanni 22 da ya fafata a gasar firimiya lig ta ƙasa, NPFL. Haka…

Read More

Wikki Tourists da Heartland na shan wuju-wuju, Rivers Utd ta zama ƙarfen ƙafa, Nwagua ya gaji Rabiu Ali – Cikakkun Alƙalluma bayan kammala wasannin mako na 3 a gasar NPFL

TangaSports A yammacin Lahadin nan ne aka fafata wasannin mako na 3 a gasar firimiya lig ta ƙasa, NPFL, sakamakon wasannin na cigaba da bada mamaki ƙwarai da gaske duba da irin yadda ƙungiyoyin gasar ke gudun yada ƙanin wani domin samun damar lashe gasar ko kuma kaucewa faɗawa ajin ƙwararru wato, NNL. Abubuwa kala-kala sun faru a ƙarshen mako kamar haka: Wikki Tourists na cigaba da ɗiban kaya a kakar bana; Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wikki Tourists ƙarƙashin jagorancin Usman Abdallah na cigaba da nuna gazawa a kakar 2020/21…

Read More

Ƙwallo 1 Ronaldo yake nema domin kafa tarihin yawan cin ƙwallo a duniya

Kyaftin ɗin ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, na gaf da kafa tarihin zama ɗan wasan da yafi kowanne yawan zura ƙwallaye a tarihin ƙwallon ƙafa. A kwanakin baya ne Ronaldo ya haura tsohon ɗan wasan ƙasar Brazil, Pele, a yawan zura ƙwallo, da ƙwallaye 758. Hakan ya nuna ɗan wasan na Juventus na buƙatar ƙwallaye 2 ne kacal domin rusa daɗaɗɗen tarihin da Josef Bican ya kafa na zura ƙwallaye 759 a wakilcin da ya yi wa ƙasashen Jamhuriyar Czech da Austria daga shekarun 1931 zuwa 1955. Sai dai cikin ƙanƙanin…

Read More

Ɗan wasan Kano Pillars Sunday Chinedu Yayi Ɓatan Dabo

TangaSports Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars ta sanar da cewa, ɗan wasan ta na baya, Sunday Chinedu, yayi ɓatan dabo. Kamar yadda ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar, Alhaji Surajo Shuaibu Yahaya yace tsawon mako biyu kenan rabon ɗan wasan da ƙungiyar ba tare da ƙwaƙƙwarar dalili ba. Alhaji Surajo yace, ɗan wasan ya buƙaci ƙungiyar da ta bashi damar zuwa gida domin duba iyalan sa a bisa dalilan rashin lafiya, kuma tun bayan kammala fafatawa wasan mako na ɗaya a gasar…

Read More

Alkalan Wasa Na Afirka Da Zasu Busa Gasar Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Duniya

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta sanar da jerin sunayen Alkalan wasanni da za su yi mata busa a yayin gasar cin kofin kungiyoyin kwallon kafa na duniya a kasar Qatar. Alkalan wasa 26 hukumar ta ware domin busa a gasar ciki harda guda 4 daga nahiyar Afirka, inda 3 su ka fito daga kasar Senegal (Ndiaye Maguette, Samba El Hadji Malick da Kamara Gabriel) sai Redouane Jiyed daga Morocco. Adadin alkalan wasa 7 ne za su yi busa a tsakiyar fili sai 12 da zasu taimaka masu. Hakazalika,…

Read More

Akwai Yiwuwar Dage Gasar Australian Grand Prix

Hukumar shirya tseren motoci ta Formula 1 a kasar Australia na duba yiwuwar dage gasar bana da tun farko aka tsara za ayi a watan Maris a birnin Melbourne a bisa sake bullar cutar Covid-19. Kawo yanzu dai ba a fara sayar da tikitin gasar ba, duk da cewa a ranar 21 ga watan Maris aka sanya ranar fara kakar bana a filin tsere na Albert Park. Ko a kakar bara ma, an soke gasar ne awanni kadan kafin farawa bayan an sami daya daga cikin ma’aikatan kamfanin Mclaren dauke…

Read More

Dalilin Ficewar Roger Federer Daga Gasar Australian Open Na 2021

Shahararren dan wasan Tennis, Roger Federer, ya yanke shawarar ficewa daga gasar Australian Open bayan tiyata biyu da akayi mar a gwiwa a lokuta mabambanta da juna. An tsawaita lokacin fara gasar bana da makonni uku zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu a bisa sake hauhawar cutar Covid-19 a kasar. Rabon Federer da fafata wasa tun a watan Janairun bara a gasar Australian Open, inda ya sami rauni a yayin karawarsa da zakaran gasar, Novak Djokovic. A bara ne dai dan Kasar Andalus, Rafael Nadal ya kamo tarihin da Federer…

Read More

Sanya Amawali Ya Zama Doka A Gasar NBA

Hukumar shirya gasar Kwallon kwando a Amurka, NBA, ta sanar da dokar fara amfani da Takunkumi ko kuma amawali ga ‘yan wasa dake jiran ko-ta kwana da masu horar dasu a yayi wasanni gasar NBA. A ranar Litinin din nan ne hukumar ta aike da wannan sanarwa ga daukacin kungiyoyin gasar kuma tuni aka fara amfani da sabon dokar a wasanni da aka fafata a Talatar nan. Sabuwar dokar tace; wajibi ne ga dukkanin ‘yan wasa dake jiran ko-ta kwana da masu horar dasu su dinga amfani da amawali kuma…

Read More